A cikin rahoton da sashen fassarar Ofishin Yada Labaran Hauza ya fitar, ya ruwaito cewa Hujjatul Islam Abdulmajid Hakim Ilahi ya bayyana haka a wani sako da ya aiko yayin wannan biki.
Cikakken Sakon Ga shi Kamar Haka:
Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai
Lallai kana kan ɗabi'a mai girma (Alkur'ani 68:4)
A munasabar cika karni goma sha biyar (shekaru duba da dari biyar) da haihuwar Manzon Allah, Muhammad Mustafa (SAWA), ina taya murna ga mallamai da ƙwararru, masana da hazikai, da kuma mabiya addinai daban-daban da ke Indiya, da kuma masu shirya wannan taro mai daraja.
Dama don Sake Karanta Saƙon Annabci Mai Dawwama
Cika karni goma sha biyar da haihuwar Annabin Rahama (SAWA) dama ce mai daraja don sake tunani da sake karanta saƙon sa mai dawwama a fannonin gina ɗan adam, ɗabi'a, adalci, da mutunta darajar ɗan adam. Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Ali Khamene'i (Dz), ya sha nanata cewa Annabi Muhammad (SAWA) ba kawai wanda ya kafa wayewar Musulunci ba ne, ya kasance shi ne mai ɗauke da tutar jinƙai, hikima, da mutunta ɗan adam na baki dayan ɗan adam.
Sirar Annabi da Zaman Lafiya a Cikin Al'ummar Indiya Mai Yawa
A cikin al'ummar Indiya mai tarihi kuma mai mutane daban-daban, wadda ke nuna misali bayyananne na zaman addinai, al'adu, da kabilu daban-daban tare, bayyana sirar Annabi zai iya taka rawar da za ta ƙarfafa zaman lafiyar al'umma, ƙarfafa mutunta juna, da kuma faɗaɗa haɗin kai tsakanin 'yan adam. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana, Musuluncin Annabi Muhammad (SAW) addini ne da ya ginu a kan tattaunawa, cika alkawari, gudanar da adalci, da mutunta ɗan adam, kuma ya nisanta kansa daga duk wani tashin hankali, tsattsauran ra'ayi, da kuma gurbata addini.
Abin Da Ya Hau Kan Malamai da Fitattun Masanan Ilmi
Ma'abota ilmi, malamai da masu bincike masu daraja, suna da aiki mai girma, ta hanyar bincike mai zurfi, bayyana hujja ta ilmi da amfani da harshe mai ma'ana, su yada ilimin Musulunci mai jinƙai da kuma sirar Annabi Muhammad (SAWA) wanda ke gina ɗan adam, da ya dace da bukatun tunanin al'ummar zamani, kuma a yaki kuskuren fahimta da gurbata addini, suna da alhakin haskakawa.
Magana ga Mabiya Addinai da Mazhabobi Daban-daban
Mabiya addinai da mazhabobi daban-daban masu daraja, abubuwan da ke tare da su na ɗabi'a da ɗan adamtaka, dukiya ce mai daraja don tattaunawa mai amfani da aiki tare na al'umma. Sirar Annabi Muhammad (SAWA), kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sha nanatawa, yana ba da samfuri bayyananne na zaman lafiya, mutunta juna, da kare darajar ɗan adam, kuma zai iya zama abin kwaikwayo ga ƙoƙarin gamayya a kan hanyar zaman lafiya da adalci.
Sako Ga Matasa da ɗalibai
Matasa da ɗalibai masu daraja, ku ne masu ba da fata ga makomar wannan ƙasa mai fadi. Ana sa ran za ku yi koyi da sorar Annabi, da amfani da shawarwari masu hikima na Babban Jagora, ku nemi ilimi, tarbiyya, ɗabi'a, ɗaukar nauyin al'umma, da kuma kiyaye asalin addini, kuma ku taka rawar gani wajen gina al'umma mai ilimi, mai zaman kanta, da kuma mai da hankali kan ɗabi'a.
Shawarwari Ga Cibiyoyin Al'adu, Addini da Ilimi
Bisa ga bikin cika karni goma sha biyar (15) da haihuwar Annabin Rahama (SAW), ana ba da shawarar: gudanar da tarurruka na ilmi tsakanin addinai bisa sirar Annabi da mutunta ɗan adam; samarwa da yada ayyukan bincike, watsa labarai, da na fasaha cikin harsunan da ake magana da su a Indiya; tsarawa da aiwatar da shirye-shiryen koyarwa da aka tsara manufa ga matasa da ɗalibai; tallafawa ayyukan jama'a a fagen neman adalci, hidimar al'umma, da taimakon marasa galihu.
Kalmar Ƙarshe
A ƙarshe, ina godiya sosai ga ƙoƙarin da malamai, masana, masu gudanar da wannan taro mai daraja, da duk ma'aikatan da suka taka rawa tare da manufa mai tsabta da tsarin haɗa kai wajen yada ilimin Annabi. Ina fatan irin wadannan shirye-shirye, a cikin hasken koyarwar Annabin Rahama (SAWA), za su kai ga zurfafa ɗabi'a, ƙarfafa haɗin kan al'umma, da ci gaban gaskiya ga al'ummar ɗan adam.
Aminci ya tabbata a gare ku
Abdulmajid Hakim Ilahi,
Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Indiya
Your Comment